“Ban-Kwana” by Ajise Vincent
A translation of “Adieu” by Ajise Vincent into Hausa by Mazhun Idris
Rantse mini, za ka zo da almuru,
Ga ni a nan tun asuba, ina ta jiran ka.
Ka sha alwashin tserar da ni daga guguwa
Ga ni a nan, na kid’ime don fakuwarka.
Mun sha shagali, a lokutan annuri,
Muna sharb’ar sautin gangar jan-hankali.
Tare da ambaliyar wak’e-wak’e da amo
Daga randar gwanayen mawak’a.
A lokacin baya, harufa sun bayi nud’uk’i
Sun haifar da jimlolin hikima, masu sa azama.
Magabatanmu sun yi dacen magada
Masu bege a annashuwar sauyi.
Yanzu ko, kaico da jimami sun sa duhu.
Kad’aici ya yi kaikomo domin sanya fata.
Rafuka masu mamako sun k’afe k’ark’af.
Saboda kai, furucina, ka tafi ba ban-kwana.
Ajise Vincent is a Nigerian Poet. His poem “Song of a Progeny” was a shortlisted poem at the Korea- Nigeria Poetry feast, 2015. His works have been published in London grip magazine, Sakonfa literary magazine, African Writer, I am not a silent poet, Poetry Pacific, Commonline Journal, Black Boy Review and various anthologies. He is currently finishing up a major in Economics at a prestigious university in Nigeria.
Mazhun Idris is a Nigerian bilingual author, multimedia content writer and freelance translator. He presently has one short story book to his name and a number of poetry lines, published across print and online media. His most recent work appeared in Sentinel Literary Quarterly.
You must be logged in to post a comment.