Now Reading
Yadda Mutum Ya Fara Tafiya A Tsaye

Yadda Mutum Ya Fara Tafiya A Tsaye

The Upright Revolution 4


Hausa

Mazhun Idris

Mutane sun kasance suna tafiya a kan k’afafuwa da hannayensu, a can zamanin baya, kamar yadda dabbobi masu k’afafu hud’u suke yi. A waccan duniyar, mutane sun fi zomo da kurege gudu; sun ma fi damisa, balle kuma karkandan.

A jikin mutum, zamanin da yake tafiya da rarrafe, K’afa da Hannu sun fi kowace gab’a shak’uwa da juna. Ba ku ga suna da kini da tamka tsakaninsu ba? Duba kafad’u ku gani. Ai sun yi daura da kwankwaso. Gwiwar hannu kuma, da gwiwar k’afa. Idon-sahu da ku’un hannu. Tsintsiyar hannu kuma da tsintsiyar k’afa. Kowannensu yana da yatsu guda biyar masu farata bi-da-bi. Hatta jerin yatsun ma sun yi asun da asun, ta yadda K’afa da Hannu ke da babban yatsa d’aya, da kuma sauran yatsu hud’u. Amma a wancan lokacin, manyan yatsu ba su yi nisa daga sauran yatsun ba. Wannan kamanceceniya tsakanin Hannu da K’afa ta kai ga suna kiran junansu da ‘ya’yan wa da ‘ya’yan k’ani, wato sako da sako.

Duk inda gangar jiki zai je, Hannu da K’afa ne suke d’aukar sa, su hud’u, da rarrafe. Tare suke kai jiki kasuwa kuma su hau da shi kan bishiya ko kan dutse, da ma kowane wajen da jiki kan buk’aci karad’awa. Ko da a cikin ruwa ma, su ke had’uwa su ba gangar jiki sukunin iyo da nink’aya. A tak’aice dai, Hannu da K’afa sun zauna ne cikin turbar Dimukurad’iyya, bisa daidaito da aiki tare. Zaman tare da sauran sassan jiki ya sa su kan nemi aron sauti daga wajen Baki, ko kuma ji, daga wajen Kunne, ko gani daga gurin Idanu.

Matsala d’aya ita ce. Sauran sassan sun fara kishin irin had’in-kan da ke tsakanin Hannu da K’afa. Sun fara jin ‘kyashin ba wa Hannu ko K’afa aron basirarsu. Kishi ya mantar da su cewa Hannu da K’afa ne suke rarrafe tare, domin jigilar d’aukansu zuwa wurare daban-daban. Ba a dade ba, sai sauran gab’ob’in jiki suka shiga kitsa tarkon raba kan Hannu da K’afa.

Harshe ne ya samo wata dabara daga gun K’wak’walwa. Wataran an wayi gari an ji shi yana ta sunbatu a fili, yana kamanta k’arfi da hikimar Hannu tsakaninsa da K’afa. Sai ya ce: waye ya fi juriya? Da jin haka, su kuma ‘yan-uwan naka, sai suka aro sauti daga gun Baki suka fara ik’irarin fifiko da musu tsakaninsu, kan wanda ya fi wani amfanar da jiki. Kafin ka ce kwabo, sai musun ya koma tankiya kan waye ya fi kyau. Hannu ya yi alfahari da sirantakar ‘yan-yatsunsu, har ya fara sukar yadda ‘yan-yatsun K’afa ke da kauri da gajarta.

Ko da K’afa ta ji saran ya yi yawa, sai ita ma ta fara mai da martani, tana kiran yatsun Hannu k’anjamammu sauran yunwa! Haka dai aka yi ta cacar-baki tsawon kwanaki, har sai da zaman doya da manjan ya kai ga kawo wa jiki tarnak’i a aikinsa. Da takun-sak’ar ya kai ga matakin gasa, kan wa ya fi tasiri, sai sauran sassan jiki suka shiga tsakanin masu tankiyar, domin yi ma su alk’alanci.

Harshe ne ya kawo shawarar shirya gasar nuna bajinta. Sauran gabb’ai suka yi kuwwar amincewa da yin wannan gasa. Wasu sun ce a tafka dambe, amma sai wasu suka ce wasan takobi ya kamata a yi. Wasu suka ce tsere ko kuma a buga dara. Ko wace gasa aka kawo, sai wasu su ce akwai k’wara ga d’aya daga cikin abokan hammayyar. A k’arshe dai, Harshe ne ya yi azancin aro hikima daga wajen K’wak’walwa ya warware matsalar cikin sauk’i. Ya ce ne a bai wa kowane d’aya, damar ya sanya wa d’ayan tsattsauran aikin da zai yi domin a gane wa zai fi bajinta. Da jin haka, sai Hannu da K’afa suka yi kuwwa suna cewa mun yarda; a shirya gagarumin taro don wannan gasa.

Da ranar gasar ta zo, suka d’unguma zuwa wata farfajiya a jeji, daf da gab’ar kogi. Kowace gab’a ta jiki ta yi shirin ko-ta-kwana, ganin cewa a yau akwai garari. Domin manyan sassan jiki, wato Hannu da K’afa za su shiga filin daga, su gwabza takara. Idanu sun yi ta wulgawa dama da hagu, ko za su tsinkayi wani abin had’ari. Kunnuwa kuwa sun nutsu ne suna sauraron kowane irin motsin da ka iya zama barazana garesu. Shi kuwa Hanci ya karkad’e k’ofofinsa ne, da shirin shak’ar duk alamar matsala wadda Ido da Kunne ba su iya ankarewa da ita ba. Ganin haka, shi kuma Harshe ya d’auki azamar k’walla k’ara da zarar ya ji matsala ta faru.

Kafin a fara takara, iska ta yad’a labarin ya zuwa duk k’uryar jejin da sararin samaniya. Kafin k’ifta ido, waje ya cika mak’il da ‘yan-kallo. Dabbobi masu k’afa hud’u ne suka fara halartowa, inda gawurtattunsu suka zo d’auke da koren ganye mai nuna cewa sun zo ne da aminci. Ba abun da kake gani a filin sai sahu-sahu na dabbobi kamar su Zaki da Damisa da Karkandan da Kura da Mugun-dawa da Giwa da Rak’umin-dawa da B’auna da Barewa da Maciji da Kurege da B’era. Dabbobin ruwa kuwa irin su Kifi da Kada da Dorinar-Ruwa sun lek’o da kawunansu ne a gab’ar kogin, don kashe k’wark’watar idansu.

Su kuwa masu k’afa biyu, wato irinsu Jimina da D’awisu da Zalbe sun yi ta fuffuka ne domin murnar wannan shagali. Sauran tsuntsaye kuwa sun yi ta wak’e-wak’e ne don taron ya k’ara armashi. Hatta k’wari ma sun yi ta kuka ne irin nasu, inda Gizo da Tana da Tsutsa suka yi ta kai-komo a fagen, da kuma kan bishiyoyi. Ita ma Hawainiya ta yi ta sand’a ne cikin taro, yayin da shi kuma K’adangare ya yi ta karakaina cikin rububi. Biri da Goggon biri sun yi ta tsalle ne a kan rassan bishiya don murna. Ko da su kansu bishiyoyi da sauran tsirrai, sun yi ta layi ne suna karkad’a ganyensu don farin-ciki.

Lokacin farawa na yi, Baki ne ya bud’e taron da rera wak’a, yana cewa:

Muna yi ne don murna
Muna yi ne don murna
Muna yi ne don murna
Soboda mu duka
Asalinmu d’aya

Da aka buga gangar fara gasa, Hannu da K’afa sun d’auki alk’awarin za su yi maraba da sakamakon gasar, duk yadda ya kaya. Kowa ya amince ba zai yi bore ko yajin-aiki ko zaman dirshan ba.

Tashin farko, Hannu ne ya k’alubalanci K’afa, inda ya watsa karare a k’asa da nufin cewa, K’afa ta kwashe kararen nan ta yi jifa da su a gani. An yardarwa da K’afa ta yi hakan ta yin aiki tare da dama da hagu ko kuma duk yadda suka ga za su iya d’aukar kararen. Ba a hana su yin amfani da yatsu d’ai-d’ai ko gwama yatsun ba, domin cin ma burinsu. Dabara dai ta rage wa mai shiga rijiya.

To amma da K’afa ta shiga fili sai abu ya gagara. Ta yi k’ok’arin ta kwashi kararen ta hanyar murginasu a k’asa da tura su gefe, da matse su tsakanin yatsu, amma abin ya ci tura. Abun da K’afa ta iya bai wuce fatali da kararen zuwa d’an nisa kad’an ba. D’aukan karare dai ya faskara!

Ko da ganin dambarwar da K’afa ta fada a k’ok’arin d’aukar kararen, sai Hannu ya aro sauti daga wajen Baki, ya k’yalk’yale da dariya, yana kuma nuna yadda hakan yake da sauk’i wurinsa, saboda sirantar yatsunsa. Hannu ya d’auki kararen cikin nishad’i ya wulwulasu a iska, ya wulla sama, ya cafe, sannan ya yi jifa da su cikin jeji. Sai aka yi ihu, taro ya d’auki shewa ana tafawa Hannu.

Ganin bajintarsa ta burge ‘yan-kallo, sai Hannu ya dulmiya cikin fage yana nuna k’arin gwanintarsa; ya d’auki shinkafa a tire, ya tsince tsakuwoyin ciki, ya kwarfi ‘yar k’asa kad’an, ya watsa sama. Sai ya d’auki allura ya yi d’inki, ya kuma d’auki igiya ya yi zarge ya d’aure kararen. Sannan ya d’auki sirin kara ya fik’e shi ya harba shi nesa. Haka dai Hannu ya yi ta irin aikin da ko a mafarki, K’afa ta san ba za ta iya ba. K’afa kuwa sai ta yi tagumi cikin k’unci, tana kallon baje-kolin fasahar Hannu, tana kuma begen irin sirantar yatsun abokin takararta. Hannayen sauran dabbobi ‘yan-kallo kuwa, sai tafi suke raf-raf, don taya d’an-uwansu murnar galabarsa. K’afa kuwa sai ta k’ara tunzura.

Zafin kaye ya sa ‘yan-yatsun K’afa yin bori a k’asa; suka yi ta birgima kamar su nutse k’asa. Amma ba a san cewa, K’afa na k’ure adakar basirarta ne wajen nemo k’alubalen da za ta sa wa Hannu, don ta rama kayin da ta sha ba.

“Me zan aringizowa wannan sarkin kurin?” K’afa ta tambayi kanta.

Da kuwwar ta lafa, sai hankali ya koma kan K’afa don ta fad’i k’alubalen da za ta d’ora wa Hannu, ta ci k’arfinsa. Da bud’e bakinta, sai K’afa ta ce, “Ai ta kwana gidan sauk’i. Abun da nake so Hannu ya aikata ai ba wata wahala ne da shi ba. Maimakon yadda jiki ke rarrafe, kawai so nake Hannu ya bugi k’irji ya d’auki gangar jiki cancak, ya kuma yawata da shi kewayen wannan da’irar.”

Sai K’afa ta zana ‘yar da’ira mai ‘dan girma a tsakiyar filin.

“Hahahaha! Ke! K’afa, sha kuruminki. Wannan har wani k’alubale ne?”

Kafin kiftawar ido, sai jiki ya yi alkafura. Sai ga gangar jiki ya yi k’ik’am kan Hannuwa biyu d’are-d’are, k’afafuwa kuma sun yi tsayuwar wata. Shi kuma Kai, ya juye k’asa, inda Idanu suka koma suna kallo sama-a-k’asa, ba sa iya gani da kyau. Da Hannu ya fara taka-taka saboda nauyin da ya d’auka, yana ta da k’ura, sai k’asa ta shiga cikin Hanci, ta sa shi atishawa.

“Atish. Atish!”

Sai taro ya d’au kuwwa, ana wak’a cikin raha ana cewa:

K’afafuwa sama lilo
Sha kuruminku
Bi su bias
Sama jannati.

Kallo dai ya koma kan Hannu, wanda d’azu-d’azu ya gama kuri da nuna bajinta, amma yanzu yana neman kasa tab’uka komai. Ko taku uku bai iya yi ba, balle ya zaga rabin da’irar da ake so ya kewaya. Sai k’ugi yake don wuya. Ba a dad’e ba sai ga jiki yana taga-taga, Hannu ya kasa jure nauyinsa, kuma sauran gabb’ai sun k’i su tagaza masa. Kawai sai ga jiki ya tintsire a k’asa, ji kake rib! K’ura ta tashi sama. Kafin k’urar ta washe, sai Hannu ya yi sauri ya sungumi gangar jiki, ya mik’e. Don ya yi balas, sai ya wawwara ‘yan-yatsunsa, ya kafa su a k’asa, don kar jiki ya sake ruftawa k’asa. Da Hannu ya nemi ya yi alkafura don ya zagaya da’ira, sai alk’alai suka k’i yarda, domin dole sai K’afa ta taimaka. K’arya dai ta k’arewa Hannu, domin k’ok’arinsa ya ci tura.

“Bwahahahah!” K’afa ta k’yalk’yale da wata irin bankaurar dariya da ta aro daga wajen Baki.

Da jin wannan muguwar dariya, sai Hannu ya fusata ya yi wani k’ugi domin ya matsa da gangar jiki. Sai dai kash! Yunk’urin bai kai ko’ina ba. Hannu ya ba da kai. Ba zai iya ba. Gangar jiki yadawo kan hud’u, irin yadda ya saba rarrafe kamar sauran dabbobi.

K’afa kuwa sai ta yi gud’a, ta shiga fage tana nuna bajintarta. Ta yi sassarfa, ta yi gudu da d’age da tsalle da sukuwa, duka ba tare da ta b’arar da gangar jiki ba. Sai taro ya kid’ime da kirari, ‘yan-kallo suna buga k’afafuwansu don taya murna. Hannu kuwa sai ya mik’e yana cewa bai yarda ba, son-kai ake nunawa. Kuma wai muzanta shi ake yi. Hannu ya manta cewa shi ne ya ce a zo a yi gasar.

Bayan da k’ura ta lafa, kawai sai ‘yan-kallo suka ankara da wani abin ban al’ajabi game da Hannu da ‘yan-yatsunsa. Sun lura da cewa babban d’an-yatsa ya ware daga sauran ‘yan-uwansa. Tun sanda ‘yan-yatsun suka rarrabu da juna, a k’ok’arinsu na cin gasa, ashe babban d’an yatsa bai dawo an had’e ba. Janyewar da ya yi ta rage wa Hannu inganci wajen aiki. Amma kafin ‘yan-kallo su fara yi wa Hannu dariya, sai suka fahimci ai kuma rarrabuwar ta k’ara wa Hannu wata hikimar ta wajen iya damk’ar abu. Kenan fad’uwa ta zo daidai da zama!

Yanzu dai an k’are gasa tsakanin Hannu da K’afa. To amma gab’ob’i da suke zaman alk’alai, sun d’auki kwanaki biyar suna jayayya kan waye ya lashe gasar. Haka dai musun ya cigaba, saboda sun gano cewa Hannu yana da b’angaren da ya yi fice. Ita ma K’afa tana da b’angaren da ta kere wa kowa. Sakamakon wannan canjaras ne ya kai ga dukkan gabb’ai sun zauna sun yi karatun ta nutsu tsakaninsu.

“Wai ma, shin mene ne jiki?” Su duka suka tambayi kansu.

Kurum sai suka ba wa kansu amsa. “Ai mu duka, mu ne jiki. Kowanenmu na buk’atar juna. Ingancin aikin ya dogara ga had’in-kanmu.”

Ganin tankiyar da ta faru tsakanin K’afa da Hannu, sai gabb’ai suka yanke shawarar cewa, idan ana son a kaucewa hakan a gaba, to ya kamata kowa ya rik’e b’angaren da ya fi fice. Kenan daga yau, gangar jiki zai rik’a tafiya ne a tsaye, bisa kan K’afa, yayin da Hannu zai zama a sama yana bugun iska. Mutum a matsayinsa na mamallakin jiki, ya yi farin ciki da wannan tsarin. To amma saboda kada a manta asalin cewa a da, mutum rarrafe yake a kan Hannuwa da K’afafuwa hud’u, duk yaran da aka haifa za su fara rarrafe ne, kafin daga baya su mik’e su fara tafiya kan k’afa biyu.

An rabawa kowa aikinsa. K’afa za ta tafiyar da jiki zuwa duk inda zai je. Amma da an isa, Hannu ne zai yi duka aikin da ake buk’atar yi, kamar d’aukar kaya da rik’e kayan aiki.

Tun daga lokacin nan, K’afa ce take yawatawa da jiki wurare. Hannu ne ke amfani da kazar-kazar d’in da yake da shi, ya yi aiki, ya kuma tabbatar da cewa abinci ya kai ga baki. Baki da Hak’ora su ne za su tauna abincin, su kuma tura shi ga mak’ogaro zuwa tumbi. Tumbi shi zai nik’e abincin ya tace mai amfani ya tura wa sassan jiki ta Jijiyoyi. Sauran tuk’ar da ta rage kuma, sai Tumbi ya aika matattarar kashi, wanda daga bisani zai zubar a cikin k’asa don inganta tsirrai. Tsirrai kuma za su girma, su fitar da ‘ya’yan itace, wanda Hannu zai tsinka ya tura wa Baki. Baki ya tauna ya tura wa Tumbi…. Haka dai tsarin rayuwa zai yi ta gudana.

Wannan rabe-raben ne ya sanya ko da a wajen wasannin motsa-jiki da raye-raye, kowace gab’a tana da aikinta. Wak’e-wak’e da Magana da dariya aikin baki ne. Guje-guje da buga k’wallo aikin K’afa ne. K’wallon Hannu da na kwando an bar wa Hannu, duk da cewa K’afa ce za ta yi guje-gujen. Wannan tsarin ne ya mayar da jikin mutum tamkar wani inji na musamman tsakanin sauran halittun duniya. Shi ya sa ma mutum kan iya cin galaba kan duka sauran dabbobi, ya kumi fi su ka’rfi da iya aiki a duniya.

Sai dai kuma, gabb’ai sun gano cewa akwai sauran rina a kaba. Wannan tsarin, har yanzu zai iya zamowa matsala. Kai, zai iya jin cewa tunda shi ne a sama, to ya fi K’afa wadda ita ce ke taka k’asa, har ma ya rik’a jin cewa shi ne jagoran sauran sassan jiki, wad’anda suke zaman bayi gareshi. Saboda haka, an yanke shawarar cewa kowa zai zama kinin kowa. Kenan idan ciwo ko farin-ciki ya samu, to za a raba shi zuwa ga duka sassan jiki, kowa ya d’and’ana. An kuma gargad’i Baki da ya san cewa yana nufin dukan jiki ne, a duk sanda zai yi magana yana cewa, “Nawa ne” ko “Ni ne.”

A k’arshe sai dukansu suka rera wannan wak’ar:

A jikin mutum
Babu bawa
A jikin mutum
Babu rago
A jikin mutum
Muna taya juna
Kowa ga kowa
Muna taya juna
Harshe ne muryarmu
Tallafeni na tallafe ka
Mu gina k’akk’arfan jiki
Tallafeni na tallafe ka
Mu gina k’akk’arfan jiki
Kyawu shi ne aiki tare

Tare muke aiki
Mu gina k’akk’arfan jiki
Tare muke aiki
Mu gina k’akk’arfan jiki
Had’in-kai shi ne k’arfinmu

Wannan wak’ar ce ta zamo Taken Jiki. Jiki yana rera ta har yau. Kuma wannan shi ne ya banbance mutum da dabbobi, da kuma duk wanda bai rungumi sauyin raba aiki tsakanin sassan jikinsa ba.

Duk da irin cigaban da sauran dabbobi suka ga mutum ya samu, ba su kwafi wannan sauyi ba. A ganinsu, yin wak’a da Baki kan yi wani abin takaici ne. Saboda ai Baki an yi shi ne domin ya ci abinci, ba ya yi wak’a ba. Sauran dabbobi sun kafa jam’iyar ra’ayin mazan-jiya, masu dogewa kan asali, tare da gujewa dukkan sauyi na d’abi’ar halittun duniya.

Domin hake ne, a duk sanda jiki ya tsaya kan bin tsarin karkasa aikace-aikace, sai ya sa mutum ya ci gaba a rayuwa. Amma duk sa’ilin da sassan jiki suka shiga takun-sak’a, to sai ya zama tamkar suna k’ok’arin ci-baya ne, da koyi da dabbobi wad’anda ke bin ra’ayin zamanin duhun-kai.

~
Read the English translation – The Upright Revolution: Or Why Humans Walk Upright by Ngugi wa Thiong’o


Mazhun Idris d’an k’asar Najeriya ne, mai rubutu da harsunan Hausa da Ingilishi. Ya wallafa littafin gajerun labaru, da kuma rubutattun wak’ok’i wad’anda aka buga a mujallu na takarda da kuma na Yanar Gizo. Aikinsa na baya-bayan nan ya fita a mujallar Sentinel.

Mazhun Idris is a Nigerian bilingual author, multimedia content writer and freelance translator. He presently has one short story book to his name and a number of poetry lines, published across print and online media. His most recent work appeared in Sentinel Literary Quarterly.

What's Your Reaction?
Excited
0
Happy
0
In Love
0
Not Sure
0
Silly
0
Scroll To Top