Now Reading
“Safaya-Taya” na Edwige-Renée DRO

“Safaya-Taya” na Edwige-Renée DRO

F20 sparewheel


Zuwa ga masoyina,

Wai mecece matsalar da ta hana ka tsaye, ta hana ka zaune. Yau mako guda kenan, kullun sai ka turomin miliyoyin sa’konni ta Whatsapp da Facebook da email, banda kiran-wayar da kake ta damuna da shi. Lallai kam, kai dai kana more fasahar sa’konnin wannin zamanin.

Abin ban-mamaki. Wai kai ne mai ce min, ka fi ‘karfin ka yi soyayya da ni. Wai ni yanzu ba nutsattsiyar yarinyar da ka sani a da ba ce. Har da cewa wai ni ba ni da sanin-yakamata, shi ya sa na ‘ki amsa maka sa’konnin da ka turo, na kuma ‘ki d’aukar wayarka duk sanda ka kira. Ahayye! Ka manta cewa kai ne ka furta cewa, kar na kuskara na tura maka rubutaccen sa’kon da za ka iya yi wa mummunar fahinta? Har kuma ka hana ni kiran wayarka, don gudun kar matarka ta gane? To, yaya kuma yanzu za ka yi ta tilo min sa’konnin waya dangane da takaicinka, da jiji-da-kanka?

Na karanta sa’konnin, kuma na ga gorin da kake min kan abubuwan da ka saya min. Ka ce kai ka saya min kayan-kanti irin na Turai, wanda ba a samu a shagunan garin Abidjan. Har ma da wayar salular da ka sai min, da kuma kwanfuta. Ka yi min gorin yawon sha’katawar da ka kai ni garin Grand-Bassam da Assinie, had’e da kud’in da ka kashe min a gidan cin-abinci, da kuma kud’in kashewar da ka yi ta ba ni. Sannan da babbansu: shagon kwalliyar da ka bud’e min. Me kake nufi da wannan gorace-goracen? Kana son na dur’kusa ‘kasa ne, na lashe maka ‘kurar takalminka da harshena?

Ka ce, ni ba kowan-kowa ba ce, sanda ka fara ganinina. Ka ce, ni ‘yar talakawa ce. Ka ce, kai ka cetoni daga ‘kas’kantacciyar unguwa mai rashin-tabbas, sannan ka wankeni da soso da sabulu, har na yi fes-fes.

Har ma ka ‘kara da cewa, “Ruwa d’auraya yake kawai, amma sabulu shi ke wanke daud’a. Kuma kud’ina ne ya sayi sabulun da ya mai da ke ‘yar-birni!”

Ka rubuta a sa’konka cewa, ba domin kai ba, da har yanzu ina ‘ku’kumin talauci; da babu mai zuwa wajena, sai talakawan samari wad’anda za su yi min burga da kyautar ‘yan-kwabbai. Ka rubuta cewa, ka zo shagonka amma na wula’kanta ka— ai na san abin da kake nufi, da ka ce ‘shagonka’.

Kana so ka ce ne, “Ai shagona ne, tunda ni na biya kud’in hayarsa.”

Wai ka san wani abu kuwa? Ina ‘kaunar sa’konninka. Rubutunka yana burgeni, musamman yadda kake rubuta abu cikin baka, domin ka jaddada wani batu. Duk sanda na karanta sa’konninka, sai na ce a raina, lallai, zurfafa karatu da cigaba da makaranta yana da kyau. Idan ba mai ilimi mai-zurfi ba, waye zai tsaya yana rubuta baka, da d’ugo da sauran ‘ka’idojin rubutu a sa’konnin wayar salula?

Na karanta inda ka tuna min da ranar da ka zo ka ba ni Sefa 100,000. Oh! Kaicona. Da a ce, na bari kud’innan sun haukata ni, har na yi birgima a ‘kasa, na kuma ce ka taka ni ka wuce fa, kamar yadda ka saba yi. Na san cewa, ka sha yaudara ta da kud’i, duk da dai a fakaice ne kawai, amma ba a gaske ba. Shi ya sa ka kasa gane cewa wayo nake maka. Zatonka ban san me nake ba, shi ya sa ma, ba ka d’aukar maganganuna da kima. Ka so na zama tamkar hoton-bango, wadda sai kana gida kake sanin mahimmancina, yayin da ka so na yi maka abin da ko matarnan Akissi Delta ba za ta iya ba.

Kai, tsaya ka ji ma. Ni fa yanzu na yanke cewa, digiri na biyu wanda na samu a kan yaudararka a gado, daga jami’arka ta cutar ‘yan-mata, ya ishe ni. Bayan shekaru hud’u na d’aukan darasi a jami’arka, tun bayan samun digirin farko, me kake tsammani zai faru? Ba zan je ga digiri na uku ba! Ka ji?

Na san wayon da na yi ta maka a kan gado ya ‘kayatar da kai. Duk juye-juye da haki da azamarnan, ka d’auka na gaske ne ko? Ka shiga tarkona, yaro. Wannan shi ake cewa iya-taku irin namu na mata. Kai ba ka lura ba, ba na surutu duk sanda ka gama zumud’inka a gado ba? Kuma ba na cewa ka tsaya, duk sanda ka ce za ka tafi? Ka d’auka ina shuru ne domin ban san kalaman da zan yabe ka ba ne, tunda ni ban yi nisa a karatun boko ba? E mana, ai ni na san maza irinka ba su da wuyar juyawa. Ahaf! Bari ka ji, duk lokacin da ka kama hanyar fita daga d’akina, ka nufi ‘kafar-bene, to ni fa komawa nake gado, bana ko ‘kara tunawa da kai.

Amma dai yanzu ban san inda ka shiga ba, wad’annan kwanakin, har ka samu sararin rubotomin sa’konni, kamar ruwan-sama. Oh, yanzu wai ka d’auka zan saurareka, duk da irin zagin da kake rubutomin? Amma babu komai. Idan haka kake so, ka yi rawarka da tsallenka. Amma fa ka sani, za ka ‘bata lokacinka ne kawai. Zan mai da kai tamakar jela ce, da ke bayana. Na gama cin amfaninka, kuma ba ni da lokacinka.

Kai, yaro! A zahiri fa ni na ci amfaninka. A fakaice fa haka ne. Ko ban hau kanka ba? Kai a gaskiya ma, idan za mu kalli abun ta wannan ‘bangaren, to ni ce na gama da kai. Sama da a ce kai ka gama da ni. Ko da kuwa ma a bad’inin ne. Ni na fad’a maka.

Ni ban san me yake ‘kona maka rai ba. Ko dai kana takaicin cewa duk da matsayinka na babban oga, wanda duk sanda aka fad’i sunansa, sai an fad’i lambobin girma da yake da su, amma kuma ga shi ka ta’ba harkar bariki da yarinya mai kwalin sakandare kawai. Haka nan dai. Ko kuma dai takaicinka shi ne, ka kasa daina ‘kauna ta. To me ne abin kunya idan ka amsa cewa haka ne. Ai dama ba zai yiwu a ce ka yi abota da mutum tsawon shekaru hud’u ba, face sai yana da matsayi a zuciyarka.

Ni ka ga ba na kunyar na ce, na ta’ba sonka. Bayan tsawon lokaci. A da zuciyata takan yi ‘kuna duk sanda ka yi tafiya. Duk kuwa da rashin iya iskancinka. Ka san me? Na ta’ba karanta tattaunawarku tsakaninka da ita! Ka tuna ranar da ka manta da wayar salularka a gidana? To ai ranar ne. Kuma ka san abin da ya sa na maka haka? To, ‘yan lokutan da ka ta’ba amsa wayarta a gabana, na ankara da yadda fuskarka kan yi annuri da kuma yadda dariyarka ta kan zamo daga zuci.

Bari ka ji yadda abun ya faru. Na cire SIM d’inka, na sa a waya ta. Kai da ka d’auka kulle wayarka da PIN code shi ne ma’kurar fasahar tsaro? Sai dai kuma, na ji ba’kin-ciki da na ga sa’konnin raha da soyayya da kuka yi a tsakaninku. Musamman ma yadda kuke zayyana tsabar madarar ‘kaunar da ke tsakaninku. Amma duk da haka ban daina sonka ba, har sai da kad’an-kad’an, kalamun rainin da kake mini suka fara barin tabo a zuciyata.

Ka tuna irin kalamun? “Ke wawuya ce. Shi ya sa ba ki iya cigaba da karatun boko ba” ka tuna fa, wannan ka fad’a ne wai kawai, domin ba ni da zurfin fahintar wani abu ne, ko da kuwa abin da bai sha min kai ba, kamar siyasar Ivory Coast.

Kai a tunaninka, na damu da ‘yan-siyasar ‘kasarnan ne irin su Bédié da Gbagbo kamar yadda ka damu da su? Kai ka d’auka na damu da menene a’kidar zaman-marina ko gurguzu. Ni abin da ke gabana shi ne samun zaman-lafiya a ‘kasarnan, domin manyan matan ‘kasarnan su cigaba da tururuwa zuwa shagona, ina samun ciniki. Ni fatana na samu kasuwar gyaran-gashi da yankan-farce da gyaran fuska da gyaran jiki da duk kwalliyar mata. Duk wani abu bayan wannan, ba damuwata ba ce. Matsalarku ta ‘yan-boko ce ta kawo mana ya’ki a ‘kasarnan. Ku kuka yi ta cacar-baki kan gurguzu da zaman-marina da yarjejeniyar mulkin-mallaka da ‘ka’idojin zama d’an-‘kasa da tsayawa za’be. Sannan kuma bayan kun cinna wutar, sai kuka ware zuwa Ghana, ‘ya’yanku kuma kuka tura su birnin Paris wajen turawan da kuka gama zagewa. Mu kuwa talakawa ba yadda muka iya, sai zama cikin wutar masifar da kuka bari, muna kallo aka kashe mana iyaye. Ka tuna fa har babana aka harbe ya mutu! Wannan shi ne dalilin barina makaranta, ya masoyina, ba domin da’ki’kancina ba ne. Ba kuma don ba na tausayin kaina ba. Ka gane???

Na san, ya kamata yanzu ka gane cewa, ni ba da’ki’kiya ce ba kamar yadda kake tunani. Kuma idan da ni da’ki’kiya ce, to da kai kuma me za a kira ka? Ka manta cewa tsotso kawai na yi maka, ka yarda aka saka sunana a takardun mallakar shagon da ka saya min?

Wata’kila ka kafe da ra’ayin cewa ni da’ki’kiya ce, saboda ba ka ta’ba zuwa shagona ba ne. Gara ma dai da ba ka ta’ba zuwa ba, domin kuwa ba zan ‘kaunaci ma’aikatana su ga yadda kake jiji-da-kai irin na ogan da ya mallaki wajen ba.

Kuma a wasi’kunka, ka ce na manne maka ne domin kai ne baitul-malina. Ko ba haka ka ce ba? To sai yaya idan hakan ne? Wata’kila ka d’auka zan zama wata ba’kauyiyar yarinya ce, wadda za ta ce ta samu aljannar duniya, domin kawai ka kaini wuraren cin-abincin da ke unguwar ‘yan-‘karya da ke Plateau. Kai, kada ka ‘dauka kai wani ubangiji ne a duniyata, iye. Wad’annan gidajen cin-abincin da ka kaini, dama na san wata rana zan shige su na sha’kata. Duk da cewa ban zaci zan kai matsayin shigarsu ba, tun ina ‘yar shekara 25. To, amma kada ka d’auka cewa kafin na same ka, ban ta’ba samun zarafin barin ‘kauyenmu Yopougon, na je garin Plateau da Cocody ba.

Kana ji na ko? Ba wai ban san cewa duk mai nufin ya sayi fili a Abidjan, kai, a ma ‘kasarnan baki-d’aya, ba zai so ya samu a Plateau ba. Kuma ka sani, ina da ‘kawaye da suka yi karatun jami’a, wad’anda nakan raka zuwa garin Cocody domin yin rijistar makaranta. Ni fa na za’bi na ‘ki yin karatun jami’a, da karatu a manyan makarantun da ake ta bud’ewa a garin Abidjan ne, kawai don ba ni da niyyar ‘barnatar da kud’ina domin neman abin da ba shi da tabbas. A gaskiya ma, ‘kawayena da muka ta’ba yin jarabawar neman shiga jami’a tare, duk da manyan ajin digirin da suka gama da shi, ga su nan har yanzu suna neman aiki a gari. Ko da wane irin aiki kuwa. Ni fa, bari ka ji. Buri na na bud’e gidan kwalliya, shi ya sa ma na je na koyi aikin.

Sai dai kai ba ka ta’ba tambayata game da wannan batun ba. Ka yi ta ‘ko’karin ka cusa min irin tunaninka. Kai ka zaci ni irin sauran ‘yan-matan garinnan ce, wad’anda suke mutuwar su samu aikin-ofis, komai rashin armashinsa. Ka zaci burina a rayuwa shi ne, kullun na ri’ka karya murya ina cewa: “ni ce sakatariyar wane.” Dama wannan ne ya sa ka gaya min cewa za ka sa abokinka, ya ba ni aikin sakatariya. Ka zaci ban gane cewa kana cika-baki ne kawai ba? Ka zaci da ka fad’a min haka, zan rungume ka, na ja ka d’aki don murna, kawai domin ka yi mini al’kawarin aiki.

Ko kuwa ka zaci, don kawai ina tambayarka jifa-jifa, game da abokinka da zai ba ni aiki, wanda kullun kake cewa za ka tuna masa, duk da kuwa na san ‘karya kake, shi ya nuna cewa na matsu da aikin ofis? Ai yadda ka d’auke ni, haka na d’auke ka. Na san idan na bi sannu-sannu, zan ci babbar gajiyarka. Kuma hakan ne ya faru, iye?

Me ya sa, a ganinka, na ‘ki yarda ka kama min hayar shago, tun farkon had’uwarmu? A ganinka ina jin dad’in zama a gidan-haya mai d’aki biyu kacal, tare da uwata da ‘kannena maza su biyu da ‘kanwata, alhalin ina ‘yar shekara 25? Ko ka zaci bana jin haushi, duk sanda na tambayi mamata ta bani 1,000 ko 2,000, sai ta bud’e baki ta ce: “Wannan samarin naki, me suke ba ki? Ko kuwa kyauta suke kwana da ke?” Sai ka ce na ta’ba kawo ma ta, ko da saurayi d’aya, balle ma ta yi zaton suna da yawa.

Ko kuwa ka yi tunanin ina jin dad’i, duk sa’ar da mahaifiyata ta kalle ni da idon jajantawa, domin cewa, ba d’aya daga cikin samarina da ya yarda ya zo gidanmu a gaisa? Ko kuma ya yarda ya ringa tallafawa gidanmu, kamar samarin wata ‘kawata, wadda ta ta’ba bai wa mamata kyautar 5,000, ko kuma wadda ta ta’ba bai wa ‘kanwata buhun shinkafa kilo 5, ta kawo gidanmu? E mana. Ai mahaifiyata ba ta damu na kawo kowane saurayi gida ba, idan dai ba wata kyauta zai kawo ma ta ba.

To lallai ba zan maka ‘karya ba. Ba’kin-cikina ya zo ‘karshe ranar da ka tsayar da motarka a bakin danja, ka le’ko da kanka waje, ka ambata kalmarnan da aka san samarin Ivory Coast da fad’a, idan sun ga wadda ta ja hankalinsu. Wato, “’Yan-mata, amma kin had’u.”

A yayin da ka nemi mu je mu sha lemu, sannan na amsa ma ka. Da sanda kuma ka ce wa mai kawo abinci, ta zo mana da gasasshiyar kaza, ai had’iyar yawu na kama yi. A gidanmu ba a faya cin naman kaza ba. Duk ranar da aka dafa naman kaza kuwa, sai mai babbar sa’a ne zai samu wata tsokar kirki. Amma, kwatsam sai ga shi ranar, wai ni ce zan ci naman kaza son-raina. Da ka lura, da ka ga na yi murmushi a lokacin da ka bayar da odar kawo kazar, sannan ka juyo ka tambaye ni, ko gasasshiyar kaza na fi sha’awar ci. Na san kai ka zaci murmushina na kunya ne. Ca’b! Ni ai ban damu wai ko kazar gasa ta za a yi, ko dafawa ko soyawa, ko ma wana irin salon girkin garin Abidjan za a yi ma ta ba. Ni kawai farincikina a lokacin, shi ne zan ci kaza.

A ranar fa ni ban yi zaton na yi babban-kamun da zan dad’e ina mora ba. Na san dai ka yi kama da mai abun-hannu. To amma, na kwana da sanin cewa idan ka ga maza masu bushasha a waje, ba za ka iya banbace tsakanin mai arziki da d’an-‘karya ba. Kowa sakin kud’i zai yi kamar gaske. Ni na yi zaton za mu ‘kare ne a gidan cin-abinci na talakawa, sannan sai ka ba ni Sefa 5,000, wataran kuma 10,000. Daga nan kuma shikenan.

Amma kuma sai ga shi, ka fara damuna, kana so ka bud’e min shago a Cocody ko Riviera, ba wai a ‘karamar unguwa irin Yopougon ba. A lokacin ne na yi wa kaina barka, na ce, “Ke yarinya, kin fa samu d’an-gaye.”

Ko da yake za ka yi mamakin jin wannan. Lallai tun lokacin ne na fara jin sonka a raina. Tabbas, haka aka yi.

Ka yi al’ajabi ko? Abin da ya faru shi ne. Na zo na fara fahimtar cewa, duk da rashin iya maganarka, duba da yadda kake d’anfaruwa da ni, tamkar wata dukiyar da ka mallaka…. Amma idan da gaske, ka d’aukeni kamar dukiyarka, to yi maza ka fitar da wannan tunanin daga zuciyarka, yanzu-yanzu! Ko da shike dai, duk da rashin kintsi irin naka, na san dai gara kai da sauran mazajen bariki. Sai dai duk da haka, ban yi sake soyayya ta rufe min ido ba. Kai ma ka san dai, ba soyayya muka zo ci duniya ba. Kuma ko da soyayya muka zo ci, ba zan yarda na karya kumallon soyayya da kai ba. Saboda na san ba ka da niyyar ka mai da ni uwar-gidanka. Don haka, me zai sa na ‘bata rayuwata don dad’ad’a maka?

Mafi kyawun abin da zan so zamowa tare da kai shi ne, bayan ka bud’e min shago, sai kuma ka kaini gidanka na zamo mai-d’akinka a garinnan. Sannan na haifa maka ‘ya’ya. Amma fa? Wannan ba shi ya fiye maka ba? Waye ya gaya maka na zo duniya cin kwaki ne? Haka ka yi nufin mayar da ni ai. Tuntuni na gano ka.

Ka fallasa kanka ne lokacin da na ambaci neman aiki, sannan ka ce min, na ‘kyale batun aiki. Har ka yi kurarin cewa, “Wane aiki kike son yi ma? Zan ba ki 50,000 duk wata, kuma zan biya miki kud’in haya da duk sauran bu’katunki.”

Ni, da wata ce, da tuni na amsa maka tayinka. Da irin matan da ka so na zama ce, ko kuma irin yarinyar ka ka yi zatona ce, da tuni na gutsuremaka yatsu don murna. Amma ka tuna wani abu, ta yi ‘karko ya fi ta yi kyau. Na riga na ri’ke maka jijiyar-wuya. Amma kai ba ka ga damar ka ri’ke ni da gaske ba. Tabbas, na gane haka ta hanyoyi masu yawa. Kai tsuntsu ne mai wayo. To, amma ka manta cewa ‘kwarya ‘yar-uwarta ‘kwarya ta ke bi, kamar yadda akushi ke bin akushi. Kawai jinka nake. Ko ma dai yaya, ya masoyin zuciyata, dama ni ban so ka ri’ki tawa jijiyar-wuyar ba. Ba yarinyar da za ta yadda ta kai tsoho gidansu, ko da kuwa da wasa ne. Ka d’auka zan bu’kaci ka zo gidanmu? To bari ka ji gaskiyar zancen.

Na san ta yiwu ka ta’ba yin zaton cewa duk sa’ar da na tambaye ka cewa, “Yaushe za ka zo gun iyayena ne?” To ina nuna na natsu da kai ne, har ya sa kake shashantar da ni da cewa, “Ai muna da isasshen lokacin. Ko ba haka ba ne?”

Hahahaha! Bari na ‘kya’kyata, ya masoyina. Ban ta’ba burin nutsuwa da kai ba har na yi tunanin aurenka. Kash, sai dai maza kamar kai, suna sha’awar su samu mataye masu soyayya da gaske. Kuna son ku yi bidirinku na bariki da yarinyar da ba ku da niyyar yin soyayyar gaskiya da ita, amma kuma kuna son ita ta so ku, so na ha’ki’ka. Kuna son ta girmama abokanku komai ginsarsu da zantukan iskancinsu. Kuna son kullun ta wage baki da hira, tana sanyaya murya. Ba kwa son ta yi muku musu. Kuma kuna son kullun ta amsa bu’katunku na yi muku ‘abubuwa’, irin ‘abubuwan’ da ba ku iya ambatonsu da baka. Kuna son ta yi muku kilakanci, amma ba irin kilakancin kawo-wu’ka ba, irin wanda zai janyo ku ce, “Ina kika koyo wannan?” Haka nan dai. Kuma kuna son ta yi muku girki. E mana, ai da iya-girki kuke auna kimar yarinya.

Ka san wani abu? Sanda na ce, “Dama na san haka za ta faru”. To ha’ki’ka na san hakan zai auku. Iye? Kuma dama na san, idan na bi sannu-a-hankali, za ka sare kuma ka ba-da-kai. Domin kuwa ai kama d’akin otal ba sau’ki ne da shi ba. Kuma a otal kana takura, saboda tsoron yin arba da idon-sani. Abidjan baban gari ne, amma kuma ba shi da fad’i. Gabad’aya duniyarma ai tsukakkiya ce. Abin da na dogara da shi kenan: wato a ‘karshe za ka sare, kuma ka rasa wani za’bi illa ka d’auki nauyin tirenind’ina a makarantar koyon kwalliya, mai tsada a garin Plateau, sannan kuma ka bud’e min shago a garin Angré. Kuma na yi amfani da irin wannan dabaranr ce, tare kuma da dakace da kuma hawayen ‘karya, kafin na samu ka bud’e min shagon. Kuma daga sannan ne, aka busa ‘kahon wargajewar abotarmu.

Dama shirina shi ne, na d’auki tsawon shekara d’aya ina gina shagona, har sai ya zama shagon da ake alfaharin zuwa a garin Abidjan. Sai kuma wata shekara d’aya, da zan fara tsara dabarun rabuwa da kai.

Hum, hum. Ka yi nazari ka gani. Ka zaci na jurewa mugunyar maganganunka da shan-kununka da ‘kazantar barikinka, kawai domin soyayya na zo yi duniya? Haba dai. Kai ma ka auna mana, ka gani!

To dai, ni yanzu zan tafi ‘kasar Togo. An d’aukeni kwangilar yin kwalliyar yan-takarar za’ben sarauniyar kyau na ‘kasar. Zan ba wa mai-gadin gidanka wannan wasi’kar a hanyata ta zuwa tashar jirgin-sama. Domin kuwa na san gidanka. Zauna a nan, wai ka zaci kai ne sarkin wayo. Sai dai kuma ga shawara zan ba ka: kar fa ka min hauka, ka je kana aika-aika, bayan ka ga wannan wasi’kar. Kar ka suskura na dawo, na ji ance ka hana ni shiga shagona. Idan ka ga dama, ka daina biya min kud’in hayarsa. Amma kada ka kuskura na dawo, na ga an fasa min shago. Domin kuwa kai zan zarga.

Na kwana da sanin cewa, ko na kai ‘kararka gun ‘yan-sanda, za ka fidda kanka. To, amma fa duk abun da ya same ni, ko ya samu shagon kwalliyata, to fa matarka za ta ji labarin abin da ke tsakaninmu. Ka dai sani, yadda matayenku na aure suke da wayewa da sanin ha’kko’kin mata, da kuma yadda za su iya ‘kwato ha’kkinsu. Mata irinmu kuka raina, kuma kuke zalunta. Amma fa, ka dai san cewa, ni ba na cikin tarkacen ‘yan-mata gama-gari. Na san inda ofisoshin ‘kungiyoyin kare ha’kkin-mata suke. Kuma ka kwana da sanin yadda mambobin ‘kungiyoyinnan na NGOs, suke da ra’ayin cewa kowace mace a Afirka ba ta da ‘karfin kare kanta daga u’kubar gallazawa ta mazaje. Don haka, ka san yadda za ku shiga fad’an, ba sassauci. Ehe!

Domin haka, ya masoyina, kamar yadda ka ce, ka gama da ni, kuma ba ka da sauran bu’katata. To ni ma haka yake a wurina. Ko ba komai, idan ba wawa ba, wa zai saurari safaya-taya, bayan ta gama yi masa amafanin da za ta yi masa?

Hausa Translation by Mazhun Idris
Originally written in French as Pneu Secours by Edwige-Renée DRO
English translation “Spare Wheel” by Edwige-Renée DRO


Mazhun Idris (@Mazhun) d’an ‘kasar Najeriya ne, mai rubutu da harsunan Hausa da turancin Engilishi. Yana wallafa ayyukansa ta hanyoyin yad’a bayanai daban-daban, kuma ya kan yi aikin fassara. Ya wallafa littafin gajerun labaru, da kuma rubutattun wa’ko’ki da dama, wad’anda aka buga a mujallu na takarda da kuma na Yanar Gizo. Aikinsa na baya-bayannan ya fita a mujallar Knot Magazine ta ‘kasar Amurka.

Mazhun Idris is a Nigerian bilingual author, multimedia content writer and freelance translator. He presently has one short stories book to his name and a number of poetry lines, published across print and online media. His most recent work appeared in The Knot Magazine.

What's Your Reaction?
Excited
0
Happy
0
In Love
0
Not Sure
0
Silly
0
Scroll To Top
%d