Now Reading
Mandela Ya Zo Ga Leah

Mandela Ya Zo Ga Leah

Hausa

Mazhun Idris

Ya ce, ‘Sam. Ƴanci bai zamowa mai ƙaidi’

Sai ƙuƙumi ya ƙaƙame daɗaɗɗe a tsibirin Robben Island.

Ta ce, ‘Sam. Ilimi bai barin wariya’ – 

Ga tabo, amma ba tsoro, fuskar Yarinyar Pakistan.

Ta ce, ‘Sam. Bangaskiya bai zamowa bisa tilas’ –

Muryar tsararriya, mai kunya amma mai kafiya a garin Dapchi,

Haskenta bai disashewa a tsakiyar masu tsattsauran ra’ayi.

Kenan, lokaci-lokaci, muryar wasici na maimaituwa –

Mandela, Malala, Leah Sharibu – hasken faɗin

‘Sam, cewar Prometheus’, haske da take,

Na samun kafa, wadda harshen wutar mai sheƙi ke fasowa ta cikin

Chibok da Dapchi, don ya sake haskaka duniya.

Read the English translation – Mandela Comes to Leah by Prof. Wole Soyinka 


Mazhun Idris d’an k’asar Najeriya ne, mai rubutu da harsunan Hausa da Ingilishi. Ya wallafa littafin gajerun labaru, da kuma rubutattun wak’ok’i wad’anda aka buga a mujallu na takarda da kuma na Yanar Gizo. Aikinsa na baya-bayan nan ya fita a mujallar Sentinel.

Mazhun Idris is a Nigerian bilingual author, multimedia content writer and freelance translator. He presently has one short story book to his name and a number of poetry lines, published across print and online media. His most recent work appeared in Sentinel Literary Quarterly.

What's Your Reaction?
Excited
1
Happy
1
In Love
0
Not Sure
0
Silly
0
Scroll To Top